Tsohuwar Matar Adam a zango ta bayyana cewar zamanta a matsayin Matar Adam a zango ya zamar Mata koma baya

Tsohuwar Matar Adam a zango Amina uba Hassan ta bayyana cewar bayan wasu shekaru da rabuwar Aurenta da jarumin kannywood Adam a zango tafara Jin sha’awar komawa harkar Fina finan Hausa.

Haka zalika ta bayyana cewar tashigo masana’antar kannywood ne sanadiyyar Marigayi Ahmed S Nuhu Kuma sun tanayin wani film dashi sau daya saidai sanadiyyar Aurenta da Adam a zango a lokacin ba’a sake wannan film din a kasuwa ba.

Saidai tsohuwar Matar Adam a zango ta bayyana kasancewarta ta taba auren Adam a zango hakan yazaman Mata koma baya domin akwai masu Shirya Fina finai damasu bada umarni dasuke tsoron sakata acikin film sabida suna tunanin hakan zai iya janyo musu matsala da Adam a zango din.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button