Jami’ar Tarayya Dake Jigawa Dutse ta karrama Lawan Ahmad (Umar Hashim) da lambar yabo

Daya daga cikin jarumai na masana’antar kannywood Lawan Ahmad Wanda ake Kira da (Umar Hashim) acikin shirin izzar so yasamu lambar girmamawa a jami’ar Tarayya dake Jigawa, Dutse.

Lawan Ahmad yasamu wannan lambar yabone sanadiyyar shirinsa Mai Farin jini Shirin izzar so, kasancewar yadda Shirin yake koyarda abubuwa da dama musamman abinda ya shafi hakuri, rikon Amana, gaskiya dadai sauransu.

Izzar so ya kasance shine shiri na farko a Fina finan Hausa Wanda yasamu lambobin yabo daga wajan kungiyoyi masu Zaman kansu Haka daga wajan malamai kasancewar yadda ake koyarda abubuwan dasuka shafi addinin musulunci acikin Shirin.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button