Yanxu Yanxu Ado Gwanda Ya saki Matarsa Maimunat Saki You innalillahi wa’inna ilaihi raji’un

Wani mummunan labari damuke samu daga masana’antar kannywood cewar shahararren mawakin Hausa ado Gwanja yasaki matarsa maimunatu har saki uku kamar yadda tashar tsakar gida ta rawaito.

Tabbas wannan shine labari mafi Muni daya faru acikin masana’antar kannywood a farkon shekarar 2022, domin kuwa babu wanda yayi tunanin cewar ado Gwanja zai iya rabuwa da matarsa maimunatu kasancewar irin shakuwa da soyayyar Dake tsakaninsu.

Inda a kwanakin baya Allah yayiwa mahaifiyar Matar ado Gwanja rasuwa kamar yadda ta sanar a shafinta na Instagram inda jaruman kannywood mazansu da matansu sukaita yimata ta’aziya saidai ba’aga ado Gwanja yayi Mata ta’aziya kokuma yasaka hoton mahaifiyar Matar tasa a shafinsa na Instagram ba domin nuna kulawa.

Haka zalika sunan Matar ado Gwanja datake amfani dashi a Instagram maisuna (Munat Gwanja) tacanjasa izuwa (pretty Munat) Haka zalika duk wani hoton ado Gwanja dayake shafinta na Instagram dinta ta gogesu gaba dayansu.

Masoyan ado Gwanja sunyi matukar alhinin wannan alamari daya faru domin kuwa lokuta da dama mawaki ado Gwanja yakan bayyana irin soyayyar dake tsakaninsa da matarsa agidajen radio idan ana Hira dashi.

Haka zalika ado Gwanja yasha fadin cewar bazai iya rabuwa da matarsa ba Haka zalika bazai iyama matarsa kishiya ba, saidai kaddara ta riga fata domin kana naka Allah yana nasa gashi yau an wayi gari ado Gwanja baya tareda matarsa Maimunat.

Saidai har izuwa yanzu Babu wani sahihin labarin abinda yasa Ado Gwanja yayiwa Matar tasa saki har uku, muna rokon Allah ubangiji yaci gaba da karewa.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button