Martanin Isa A. Isa Bayan kotu ta yankewa sadiya haruna hukuncin Zaman gidan yari na wata shida akan kazafin datayi Masa

idan masu karatu suna bibiyar shafinmu na arewajoint munkawo muku cikakken rahoton yadda alkali ya tasa keyar sadiya haruna izuwa gidan maza harna tsawon watanni shida bisa laifin da aka kamata dashi.

A cikin rahoton dai Mai Kara jarumin kannywood Isa A. Isa Yana karar sadiya haruna Kan Bata mishi suna datayi na kiransa da (Dan luwadi) tareda cimai zarafi a shafinta na Instagram shekara biyu baya dasuka wuce.

Inda acikin bidiyon Isa A. Isa ya bayyana tun wannan lokacin Daman suna kotu shida ita saiyanzu cikin hukuncin ubangiji aka Gama Shari’ar inda sadiya haruna ta amsa laifinta tareda Karyata munanan kalaman data fada akan Isa A. Isa a shafinta na Instagram.

Cikin wani bidiyo da jarumin kannywood din ya Fitar Isa A. Isa yayi matukar godiya ga Allah akan sakayyar da Allah yayi Masa, Haka zalika ya godewa masoyansa wanda yasani dama wanda baisansu ba Kan yadda suke tayasa murna akan samun nasara a wannan Shari’ar da akayi tsakaninsa da Sadiya Haruna.

A gefe guda Kuma wasu sun matukar tausayawa Mai Saida Kayan Mata sadiya haruna kasancewar irin yadda halinda Zata tsinci kanta aciki wanda Bata taba shiga irinsa ba, gadai cikakken bidiyon jarumi Isa A. Isa

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button