Mijina baimun saki uku ba amman dai bana gidansa yanzu Haka ina gidanmu cewar Matar Ado Gwanja

Acigaba dagano cikakken labarin rabuwar auren mawaki Ado Gwanja da Mai dakinsa maimunat, wasu hujjoji sun Kara bayyana daga bangaren guda biyu Wanda mutane zasu gamsu dashi akan labarin sakin da aka bayyana cewar Ado Gwanja yayiwa Matar tasa.

Cikin wata tattaunawa da matar ado Gwanja maimunat tayi da Tashar tsakar gida a shafin sada zumunta na Instagram ta bayyana cewar mijinta baiyi Mata saki uku ba kamar yadda mutane suketa yadawa a kafofin sada zumunta na zamani.

Saidai maimunat ta bayyana cewar sun samu Yar matsala tsakaninta da mijin nata wanda a halin yanzu haka tana gidansu da zama, ma’ana bata gidan ado Gwanja din.

Maimunat ta Kara da cewar tabbas akwai kauna da Soyayya tsakaninta da mijinta wani tsautsayi ne ya gifta tsakaninsu wanda insha Allah Nan bada jimawa ba zasu sasanta tsakaninsu domin Takoma cikin gidan mijinta.

Tabbas duk wani Mai bibiyar shafukan sada zumunta zai tabbatar da cewar yadda ado Gwanja da matarsa maimunat suke nunawa juna Soyayya bazaka taba tunanin wani alamari Mara Dadi zaishiga tsakaninsu ba, saidai komai kaddarace daga Allah.

A gefe guda bayan tuntubar mawaki Ado Gwanja Kan labarin jita jita na cewar yayima matarsa saki uku shin gaskiyane, Ado Gwanja ya bayyana cewar Shi Bai saki Matarsa ba, amman dai a halin yanzu bata gidansa, saidai bazai iya fadawa masoyansa labarin abinda yashiga tsakaninsu ba domin wannan maganar cikin gida ce.

Masoyan Ado Gwanja sunyita bayyana ra’ayinsu a kafofin sada zumunta gameda wannan mummunan labarin inda sukaita addu’ar Allah ubangiji ya daidaita tsakaninsu shida matarsa.

Gawani gajeran video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button