Sababbin Hotunan Rahama Sadau rungume dawani darakta kudancin najeriya ya janyo cece kuce

Wasu hotunan fitacciyar jarumar kannywood Rahama Sadau wanda ta wallafa a shafinta na Instagram a jiya sun janyo cece kuce kasancewar yanayin yadda tadauki hoton manne dawani daraktan Fina finan kudancin najeriya.

Saidai wasu suna ganin jaruma Rahama Sadau bata dauki irin wannan hotunan a matsayin komai ba kasancewar a kwanakin baya dasuka wuce anga jarumar ta wallafa wasu hotuna tareda wani jarumin Fina finan kudancin najeriya na Nollywood a shafinta na Instagram.

Saidai Jim Kadan bayan kwana daya tacire hotunan, Haka zalika a wancan karon Rahama Sadau din Bata bayyana dalilinta na cire wannan hotunan a shafinta na Instagram ba.

Rahama Sadau dai fitacciyar jarumace acikin masana’antar kannywood saidai a shekarar data gabata andakar da ita sanadiyyar wata shiga datayi wanda har hakan ya fidda tsaraicinta inda wani yaje kasan hoton yayi batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad s.a.w

Saidai a gefe guda wasu masoyan jarumar suna goyan Bayan irin wannan hotunan datake dauka Haka zalika a dayan bangaren masoyan nata suna Allah wadai da irin wannan hotunan dasuka sabawa alada da addinin musulunci baki daya.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button