Sarkar Gwal ta Naira Miliyan 11 da Hafsat Idris tasaka ranar sunan jikarta ya janyo cece kuce

Idan baku mantaba a shekarar data gabata wato shekarar 2021 akayi auren babbar diyar hafsat Idris acikin garin Kano, shagalin daya samu halartar manyan jaruman kannywood da kanana.

Inda acikin wannan Makon Hafsat Idris ta wallafa wani gajeran bidiyo a shafinta na Instagram rike da jariri a hannunta inda ta bayyana cewar Allah ya azurta yarta da samun ya mace ma’ana hafsat Idris tasamu jika mace, Kuma an radawa Yar sunan hafsat.

Saidai wani alamari ya matukar daukar hankalin mutane wato sarkar Gwal dinda jarumar kannywood hafsat Idris tasaka ranar sunan jikar Tata na kimanin naira miliyan 11 kamar yadda jaridar labarun hausa ta rawaito ya matukar janyo cece kuce.

Mutane sunyita bayyana ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta kasancewar irin yanayin Rayuwar matsi da wahala da alumma suke ciki, masoyan jarumar suna ganin wannan almubazzaranci ne da kudi.

Saidai a gefe guda Kuma masoyan jarumar suna ganin danta saka sarkar Gwal ta kimanin naira miliyan 11 bawani abun magana bane kasancewar wata babbar jarumace Kuma Yar kasuwa Dan Haka abun baizama abin cece kuce ba.

Haka zalika har izuwa yanzu fitacciyar jarumar batayi wani tsokaci gameda maganganu akan sarkar Gwal din naira miliyan 11 data saka ba, gadai wani gajeran bidiyo shagalin yadda aka Gudanar da sunan.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button