Wani masoyin jarumar kannywood Nafisat Abdullahi ya rera Mata Waka a shafin tiktok

Kamar yadda Kowa yasani akwai masoyan jaruma kannywood maza da Mata Wanda zakaga suna matukar Ƙaunar jaruman, wasuma zakaga har kwaikwayon irin shigar jaruman sukeyi sabida kauna.

Anan gefe guda Kuma Wani matashinr a shafin tiktok masoyin jaruma Nafisat Abdullahi, inda wani yacemai indai yacika cikakken masoyin Nafisat Abdullahi to ya rera Mata waka a shafin na tiktok.

Ai kuwa hakan akayi inda wannan Saurayi yafara rerawa jarumar kannywood Nafisat Abdullahi waka kamar yadda sauran mawaka sukeyi saidai wakar yayitane da baki kawai, ma’ana Babu kida cikinta.

Wannan dai ba sabon alamari bane domin kuwa akan samu masoyan jaruman kannywood dasuke zuwa daga wasu garuruwa domin su hadu kawai da jaruman na kannywood.

Inda a shekarar data gabata akwai wani Saurayi matashi daya Zo tundaga Jahar yobe izuwa Jahar Kano domin yaga Maryam Yahaya inda akai rashin sa’a baiga jarumar ba, bakin ciki yasa jarumin yasha fiya fiya domin hallaka Kansa da taimakon mutane Bayan ya Fadi aka daukesa izuwa asibiti domin ceto Rayuwarsa.

Hakan ya taba faruwa da mawaki Ali jita inda wani Saurayi shima yataso tundaga nisan duniya yazo Jahar Kano domin ya hadu da mawakin Kuma cikin hukuncin ubangiji ya hadu da mawaki Ali jita, gadai cikakken wakar da masoyin Nafisat Abdullahi yayi Mata.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button