Ali Nuhu da Falalu A Dorayi Sun Karyata Ladin cima Kan cewar dubu N2,000 ake Bata idan tayi film

Ana cigaba da cece kuce Kan irin kalaman da jarumar kannywood tayi ladin cima na cewar idan tayi film daga dubu biyar zuwa Kasa ake biyanta har dubu biyu ana bata idan tayi film.

Fitaccen jarumin kannywood Ali Nuhu ya bayyana cewar kalaman Ladin cima datayi akwai kuskure acikinsu sosai domin koshi a kwanannan datayi Masa aikin shirinsa maisuna “ALAQA” naira dubu arba’in yabata 40k.

Sarki Ali Nuhu yakara da cewar zagin da Yan Kwallo sukeyiwa jaruman na kannywood bazaiga laifinsu ba domin basusan asalin Gaskiyar yadda abubuwa suke tafiya ba.

Rahotanni sun bayyana cewar Kwanannan A Set Din Gidan Badamasi Na Falalu Dorayi Hadiza Gabon Taji Ladin cima tana labarin Zata Saya gida Amman batada cikon kudin sayan gidan inda Hadiza Gabon taje Mota tareda dauko zunzurutun kudi naira dubu dari uku 300k, Haka ladin cima ta fashe da Kuka tareda yin godiya was jarumar kannywood Hadiza Gabon.

Sannan Da Azumi Hadiza Gabon Ta Kara Saka producer Naziru Dan Hajia Ya karbi Account Number Ladin cima inda ya turawa Hadiza ta turawa da jarumar kudi domin tayi bukatunta dasu.

Haka zalika an bayyana cewar a lokacin da ake daukar cigaban Shirin gidan Badamasi Kudin Da Falalu Dorayi ya bawa Ladin cima ya wuce 30k Sannan Aikin datayi baikai wannan kudaden da aka batana.

Mutane sunataci gaba da cece kuce a shafukan sada zumunta musamman Facebook da Instagram Kan irin kalaman da jaruma Ladin cima tayi na cewar idan tayi film kudinda ake baita baya wuce dubu biyu ko dubu hudu zuwa dubu biyar, Allah ubangiji ya kyauta.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button