Tirkashi Masana’antar kannywood Takama da wuta biyo Bayan kalaman Ladin cima nacewar dubu 2 zuwa dubu 4 ake Bata

Masana’antar kannywood tanacigaba da kamawa da wuta kasancewar yadda producers da directors daga cikin masana’antar kannywood suke fitowa domin Kare masana’antar tasu tareda martani Mai zafi akan kalaman da naziru sarkin Waka yayi akansu.

Rigimar dai tasamo asaline tun lokacin da shafin BBC Hausa suka saki hirarsu dasukayi da daya daga cikin iyaye jarumai Mata na masana’antar kannywood Ladin cima inda ta bayyana cewar tun lokacin data farayin film izuwa yanzu ba’a taba bata sama da naira dubu biyar ba.

Lamarin Dayasa sarki Ali Nuhu da Falalu A Dorayi Suka bayyanawa BBC Hausa cewar sun taba biyanta kudi sama da abinda tayi ikirarin cewar ba’a taba bataba.

Inda sarki Ali Nuhu ya bayyana cewar a kwanannan acikin shirinsa maisuna “ALAQA” ya biya ladin cima kudi naira dubu arba’in N40,000 Haka zalika Falalu A Dorayi yace acikin Shirin Gidan Badamasi ya biya Ladin cima kudi naira dubu talatin N30,000.

Wannan Dalilin yasa naziru Sarkin Waka yafito ya kalubalanci masana’antar tareda Jan hankalin producers da directors cewar suji tsoron Allah sudinga adalci wajan biyan mutane hakkinsu.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button