Wallahi Yan kannywood kuji Tsoron Allah kudinga biyan mutane hakkinsu cewar naziru Sarkin Waka

Biyo bayan yadda jarumar kannywood ladin cima ta bayyana cewar tunda take acikin masana’antar kannywood ba’a taba biyanta kudi sama da naira dubu biyar ba acikin wata Hira da gidan jaridar BBC Hausa tayi da ita.

Saidai wannan maganar ta matukar tada Kura inda naziru sarkin Waka yafito cikin fushi yayi raddi Mai zafi tareda bayyana cewar yakamata Yan masana’antar kannywood suji tsoron Allah sudinga biyan mutane hakkinsu.

Haka zalika Jarumi sarki Ali Nuhu da Falalu A Dorayi sunfito sun Kare kansu inda Jarumi Ali Nuhu ya bayyana cewar ko acikin shirinsa na karshen Nan maisuna “ALAQA” ya biya Ladin cima kudi naira dubu arba’in duk da kuwa aikin datayi baikai na wannan kudin ba.

Haka zalika Jarumi Kuma darakta Falalu A Dorayi yafito ya bayyana cewar acikin Shirin Gidan Badamasi ya biya Ladin cima kudi naira dubu talatin.

Izuwa yanzu dai mutane sunata korafi tareda cece kuce a shafukan sada zumunta inda ake ganin cewar masana’antar suna danne hakkin wasu daga cikin jarumai, inda a gefe guda wasu suka fito suka Kare kansu tareda Kare masana’antar akan kalaman da Ladin cima tayi.

Gadai cikakken bidiyon da naziru sarkin Waka yayiwa masana’antar kannywood zazzafan martani.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button