Barazana Naziru sarkin Waka yakeyi saimunga yabada naira miliyan biyu zuwaga ladin cima zamu yadda

Biyo Bayan irin rikicin daya faru acikin masana’antar kannywood Kan kalaman da naziru sarkin waka yayi akan cewar masu Shirya Fina finai damasu bada umarni suji tsoron Allah wajan biyan hakkin mutane haka zalika sudaina cewar saisunyi lalata da mace kafin su sakata acikin film.

Inda wannan maganar tajanyo cece kuce, wasu da dama daga cikin masana’antar kannywood sunyiwa naziru Sarkin Waka zazzafan martani Kan irin kalaman Daya fada akansu Harda kungiyar Jarumai Mata na masana’antar kannywood din.

Saidai jiya naziru Sarkin Waka yafito yayi wani bidiyo inda yake bawa mutane hakuri akan kalaman dayayi, Kuma ya bayyana cewar bawai yayi Haka bane domin yaci zarafin wani kokuma wata acikin masana’antar kannywood.

Cikin jawabin nasa naziru sarkin waka yace shida Yan uwansa sun yanke shawarar zasu bawa Ladin cima naira miliyan biyu domin taje taja jari Takama Sana’a, Haka zalika tsohuwar jarumar kannywood Fati slow data fito tayi munanan kalamai akansa shima yace yabarta da Allah itama ta turo wakilanta su karba Mata naira miliyan daya taje taja jari takama Sana’a.

Saidai wasu mabiya shafukan sada zumunta sun bayyana cewar bazasu yadda da maganar naziru ba harsai sunga yabawa Ladin cima kudi naira miliyan biyu ya nunawa duniya Kowa yagani, a cewarsu domin naziru Sarkin waka yasaba irin wannan alkawarin daga baya Kuma yaki zuwa yacika alkawarin.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button