Allah sarki kalli abinda yafaru da Fati slow bayan Naziru Sarkin Waka yabata kyautar miliyan daya

Masha Allah bayan alkawarin da fitaccen mawaki naziru Sarkin Waka yayi na cewar zaibawa tsohuwar jarumar kannywood naira miliyan daya naziru Sarkin Waka yacika wannan alkawari inda ya tura da kudin tacikin account din jaruma Mansurah isah.

Saidai tun bayan bawa Fati slow wannan kudin wasu daga cikin aminai da kawayen Fati slow sunata kokarin ganin saisun samu wani Abu acikin wannan kudin.

Inda Mansurah isah tayi wani rubutu a shafinta na Instagram jiya inda take gargadin masu nuna cewar sunaso Fati slow tabasu wani abu acikin kudinda naziru Sarkin Waka yabata da cewar su shiga hankalinsu Kuma duk wanda yake ganin ya isa yabiyo Mansurah isah gida da sunan yazo karbar kasonsa yaga Mai zaifaru dashi.

Inda Mansurah isah ta bayyana cewar zatayi kokari wajan ganin ta daura tsohuwar jarumar kannywood din Fati slow akan hanya madaidaiciya ta yadda zata Fara harkar kasuwanci ta batareda wani matsala ba.

Munayiwa tsohuwar jarumar kannywood Fati slow addu’ar Allah ubangiji yasa wannan kudaden sune silar arzikinta.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button