Allah sarki – Dauda kahuta Rarara yakai Ta’aziyar Marigayi Nura Mustapha waye Daraktan Shirin Izzar so
Allahu akbar akwana atashi babu wahala Allah ya karbi rayuwar marigayi Nura Mustapha waye a ranar lahadi 02/07/2022 wanda mutuwar Marigayi Nura Mustapha waye ta matukar dagawa alumma hankali.
Shima mawaki Dauda kahuta Rarara yakai Ta’aziyar gaisuwar rasuwar Nura Mustapha waye Daraktan Shirin Izzar so zuwa ga Mahaifiyarsa da iyalansa anan cikin garin kano tareda rakiyar wasu daga cikin ma’aikatansa.
Rasuwar Nura Mustapha waye ta matukar jijjiga masana’antar Kannywood kasancewar yadda kowa ya shaidi Marigayin yake mu’amala da kowa lafiya haka zalika an bayyanasa a matsayin mutum mai nagarta da ganin girman nagaba dashi.
Aminin marigayin Lawan Ahmad ya bayyana rasuwar Nura Mustapha waye a matsayin babban rashi ga masana’antar Kannywood inda ya bayyana cewar Kannywood bata tabayin rashi kamar wannan ba.
Ga bidiyon gaisuwar da Dauda kahuta Rarara yakaiwa iyalan marigayi Nura Mustapha waye
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.