Allahu Akbar – Yau Shekaru Tara Cif-Cif (9) Da Rasuwan Marigayi Umar Abdulaziz Fadar Bege

Umar Abdul Aziz Fadar Bege Shahararren Mawakin Annabi Muhammadu (SAW) Cikin Harshen Hausa Wanda Muryan Sa Ya Karade Ko’ina A Fadin Duniya Musamman Africa.

Fadar Bege

Fadar Bege Matashi Ne Wanda Ya Bada Gagarumin Gudumuwa Wurin Yada Soyayyan MANZON ALLAH SAW A Zukatan Al’ummar Musulmi, Allah Ya Masa Baiwar Isar Da Sakon Musulunci Cikin Hikima Tare Da Nusar Da Masoya Kara Soyayyan Alhul Bait Da Waliyai.

Umar Abdul Aziz Fadar Bege Kafin Ya Fara Kasida Ya Kasance Mai Sana’a A Kowanne Lokaci, Yayi Karatun Addini Dana Zamani Inda Daga Baya Ya Shigo Birnin Kano Don Fadada Karatun Sa Na Addinin Islama.

Kafin Rasuwar Sa Yayi Wakokin Yabon Manzon Allah SAW Wanda Ba’asan Adadin Saba, Kuma Ya Shahara A Yammacin Africa Musamman Najeriya, Mutum Ne Mai Himma Da Kokari, Duk Wanda Yayi Mu’amala Dashi Sai Ya Yaba Da Hali Irin Nasa.

An Haife Shi A Shekara Ta 1974 Yayi Wafati A Shekara Ta 2013 Sanadiyyar Rashin Lafiya. An Masa Makwanci A Makaranta Dake Birnin Kano A Najeriya. Yabar Mata Da Yara Biyu.

Wasu Daga Cikin Wakokin Da Yayi.

 • Takalminka Yafi Kowa
 • Labbaika Rasulillah
 • Farkon Mafadi,
 • Aahalan Wassahalan,
 • Ya Mustapha Zuljudi,
 • Assalamun-Alaika,
 • Dan Asali,
 • Maula Inyass,
 • Lamuni Nake Nemah,
 • Nagaban Hankali,,
 • Murhun Gidan Annabi,
 • Mai Cikar Asali Ne,
 • Mai Babban Masallaci,
 • Mahamudu Ma’aiki Na,
 • Annabi Ni Ina Gaida Kai,

Allah Ya Jaddada Masa Rahma Ya Gafarta Masa Allah Ya Sadashi Da Manzon Rahma SAW. Allah Yasa Aljannah Ce Makomar Sa, Amiin

Daga: Babangida A. Maina
Founder/MD Tijjaniyya Media News
Allah ubangiji yakai haske kabarinsa

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button