Yanzunnan Dan Takarar Gwamnan jihar Katsina Allah yayi Masa Rasuwa Innalillahi wa’inna raji’un
Gabanin karatowar zaben shekarar 2023, Allah ya karbi rayuwar daya daga cikin yan takarar gwamna a jahar katsina.

Allah ya yi wa ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarkashin jam’iyyar PRP, Alhaji Bashir Lawal Yar’adua rasuwa.
Marigayi Alhaji Bashir Lawal Yar’adua shi ne mai kamfanin Hajara Farms, ya rasu a Abuja a daren jiya Litinin bayan gajeruwar rashin lafiya.
Allah Ya jiƙansa da rahama, amin.
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.