A karon farko kalli video Yadda Nura M Inuwa ya fadi Yadda aka watsamai Acid a fuskarsa
Mawaki acikin masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood Nura M Inuwa cikin wata hira da akayi dashi a gidan jaridar BBC Hausa ya bayyana asalin yadda aka watsa mishi Acid a fuskarsa.
Nura M Inuwa shahararren mawakin hausa ne wanda yayi suna aciki dama wajan Najeriya ta hanyar rera wakar hausa, yana wakokin Aure, siyasa dakuma wakokin da ake sakawa acikin film.
Nura M Inuwa ya bayyana cewar wata rana an kirasa da wata number akacemai anaso zaiyi wakar aure ne kuma mutanen dasuka kirasa sunce daga garin Abuja sukazo, sun fada mishi sunje studio nasa ance bayanan.
Sai suka shirya inda zasu hadu Mawaki Nura M Inuwa ya dauki kafarsa izuwa wajan dasuka shirya, zuwansa keda wuya kuwa suka dauko wani abu suka watsa mishi a fuskarsa acewar nawaki Nura M Inuwa.
Ga cikakken bidiyon hirar da akayi dashi
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.