‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗalibin Kwalejin Ilimi Ta Tarayya Dake Katsina A Yawon Sallah
Daga cikin waɗanda ‘yan bindiga-daɗi suka kai wa farmaki a yayin dawowa daga yawon Sallah a cikin birnin Katsina, hada ɗalibin Kwalejin Ilimi Ta Tarayya da ke Katsina (FCE Katsina), ɗalibin mai suna Anass Adamu.

Shi ne wanda ya rasa r@nsa yayin gudun tsira daga wajen ‘yan bindiga-daɗi a hanyarsu ta komawa Ƙaramar Hukumar Jibia.
Ɗalibin mai suna Anass Adamu ya kammala karatunsa wanda yake a sashen SOS a lambar karatu ta (41Series), wanda har yanzu ba ma a fara ba ‘yan lambar karatunsu result ba, ɗalibin dai yana zaune tare da mahaifansa a Ƙaramar Hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Allah ubangiji yaji kansa da Rahama Amin.
Daga Zaharaddeen Gandu
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.
