Labarin Mutuwar Ali artwork karyane domin yananan da ransa bai mutu

Tun cikin daren jiya dai aketa wallafa labarin mutuwar fitaccen jarumin barkwancinnan wato Ali artwork cewar Allah yayi masa rasuwa.

Wannan labarin ya matukar tayar da hankalin masoyansa harma da wanda ba masoyansa ba domin maganar mutuwa akeyi, kuma mutuwa ba abun wasa bace.

Inda wani shafi maisuna “Debit.ng Hausa” dake Facebook suka wallafa hoton Ali artwork tare da yin rubutu a kasa wanda ke bayyana cewar Allah yayiwa jarumin rasuwa kamar yadda kuke gani.

Saidai bayan dogon bincike damukayi dakuma jin tabakin nakusa da jarumin sun bayyana cewar suma haka sukaga wanann labarin yanata yawo a kafar sada zumunta kuma labarin bashida tushe.

Wannnan dai bashi bane karo na farko da ake wallafa labaran karya akan wasu jaruman cewar sun rasu alhalin sunanan da ransu basu mutu ba, Allah ubangiji ya kyauta.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button