Mu Tausayawa Safara’u A Matsayin Ta Na `Yar Uwar Mu Musulma cewar Abubakar A Adam Babankyauta
Wani matashi maisuna Abubakar Adam ya bayyana cewar yakamata a tausayawa Safara’u a halin data tsinci kanta bawai ayi mata dariya ba.

Tabbas akwai abun ban takaici da bakin ciki mai cike da dacin zuciya a ce kaga musulmi ko musulma suna kokarin zama ribar shedan a nan doran duniya.
Abun ban takaicin ma shine irin yadda harkar fina finan hausa ta lalata tarbiyar wasu ya
yan musulmai kuma hausa fulani irin su Safara’u da dai sauran ire – iran su.
Ya zama dole akan mu musulmai mu tausayawa duk wanda muka ganshi a cikin wani yanayi wanda yaci karo da koyarwar addinin musulilci badon komai ba sai dan kallan yadda mako marshi zata kasance idan har ya koma ga Allah a haka.
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.