Yanzunnan Yan Bindiga suka kashe wani Matashi a garin Katsina Innalillahi wa’inna raji’un

A Daren Jiya Asabar Ƴan Bindiga Dauke Da Bindigogi Suka Kai Hari A Garin Tsagero Dake Cikin Karamar Hukumar Rimi A Jihar Katsina Inda Suka Hallaka Wani Matashi Har Lahira, Badamasi Rabe, Wanda Aka Fi Sani Da (Bosi) Har Lahira.

Majiyar RARIYA Ta Shaida Mata Cewa Ƴan Bindigar Sun Shigo Cikin Garin Tsagero Da Misalin Karfe 2:30 Na Daren Jiya Asabar, Bayan Sun Kashe Bosi Dake Sana’ar Kayan Gwari, Sun Kuma Tafi Da Wata Kurkura A Garin.

Tuni Dai Aka Yi Jana’izarsa Kamar Yadda Addinin Musulunci Ya Tanada A Garin Tsagero Dake Karamar Hukumar Rimi A Jihar Katsina Da Safiyar Yau Lahadi.
Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button