Daga karshe dai jaruma Fati washa ita zata Maye Gurbin Nafisat Abdullahi acikin shirin Labarina

Bayyana fuskar Fati washa awajan daukar cigaban shirin labarina ya bayyanawa duniya cewar itace zata maye gurbin jaruma Nafisat Abdullahi acikin shirin bayan sanarwar da Nafisat Abdullahi tayi nacewar baza’a sake ganin fuskarta acikin shirin ba.

Shirin labarina yana daya daga cikin fina finan hausa masu dogon zango wanda sukeda dubban makallata a fadin duniya kasancewar yadda shirin yakeda inganci kuma yana fadakar tareda nishadantar da makallata shirin.

Saidai tunda Malam Aminu saira ya wallafa wani gajeran faifan bidiyo Fati washa a inda ake daukar shirin labarina hakan yasa yan kallo sukaita nuna farin cikinsu ganin cewar tabbas jaruma Fati washa itama zata taka babbar rawa acikin shirin labarina.

Inda ayanzu dai makallata shirin labarina suna zaman jiran dawowar shirin a watan agusta wato 8/2022 inda ya bayyana cewar shirin zaicigaba da zuwa tsakanin 12/08/2022 kokuma 15/08/2022.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button