Sheik Abduljabbar Ya Roki Alkalin Alkalai daya dauke shari’arsa daga Gaban kotun shari’ar musulunci zuwa wata kotun daban

A zaman kotun na wanan Rana Shekh Abduljabar Nasir kabara ya Roki Alkalin Alkalai da ya dauke wanan sharia daga gaban babbar kotun sharia musulunci dake kofar kudu karkashin Mai sharia Ibrahim sarki Yola.

A kaiwa wani alkalin Wanda bashi da kowace irin Alaka da Wanda suke Kara.

Abduljabbar kabara yayi zargin cewa tun farkon shari’ar anyi masa alkawarin bashi Dama da gabatar da bayanai a ishashen lokaci .

Haka Kuma kan Batun rubuta rikodin da akeyi a gaban kotu Ina Ganin sauye sauyen wasu abubuwan idan na nemi kofi na sharia Kuma a gaban kotu na tashi da nufin nayi bayani da Neman a gyara Kai alkali kahauni da fada ni Kuma Inajin tsoron Hakan kada nasaka ka fusataka Hakan tasa naja bakina naishiru.

Kuma ana hanani gabatar da bayanai na yadda nake bukata

Kuma a zama na karshe da akayi lauyan gwamnati a irin tambayoyin da yakeyimin ya shiga wasu bayanai na kwace da Zina Kuma bayan Bai taba tambayata akan kunshin tuhumar da akeyimin ba.

Haka Kuma a zaman da ya gabata lauyana ya nemi Jin ba’asin da yasa Lauyoyin Gwamnati suka tsalake wani Batu a lokacin da suke gabatar da tambayoyinsu ga reni ,sai alkali kayiwa lauyana tsawa Kuma wanan ya bani tsoro don haka na nemi alkalin alkalai ya Sauyamin wata kotu, wadannan sune kadan daga cikin Dalilaina na rokon a canjamin wata Kotun.

Kotu ta tamabayi malam abduljabar kabara Mai zaisa baizai Fadi Dalilain nasa gaba Daya ba?

Malamin yaka da baki yace iya Hakan sun wadatar.

Lauyan gwamnati barista surajo sa’ida SAN ya roki Kotu da ta dage wanan zama Kuma a nemi lauyansa yazo yayi bayanin rashin zuwansa
Saboda haka mu bazamu mayar da martani ba har sai lauyansa yanan.

Kotu ta bayana cewa lauyan Yana sane yaki zuwa gaban kotu domin kawo tsaiko akan wanan sharia don haka Wanda ake Kara ya sanar da shi cewa Ranar da za’a cigaba da wanan sharia domin ya cigaba da aikinsa.

Amman Idan barista dalhatu shehu Bai zoba kotu zata chanza wani lauyan na daban domin kotu ba zaman kowa takeyi ba, zaman doka take.

Bayan fitowa daga kotu Wakilanmu Nazifi Bala Dukawa da Usaini jibrin gwammaja suka nemi jin ta bakin Lauyoyin Gwamnati inda sukace bazasuyi magana da Yan jarida ba.

Daga karshe Alkalin Ya Sanya Ranar 28 ga watan da muke ciki domin cigaba da Sauraren shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button