Shugaban Tace fina finai ta jahar kano Afakallahu zaiyi WUFF da Tsohuwar jarumar Kannywood Rukayya Dawayya
Isma’ila Na’Abba Afakallahu na shirin auren tsohuwar jarumar Kannywood, Rukayya Dawayya kamar yadda alamu su ka nuna.
Afakallah shi ne shugaban hukumar tantance fina-finai ta Jihar Kano kamar yadda Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya nada shi. Shafin LH ne ruwaito.

A lokacin, gwamnan ya ce ya nada shi ne don ganin ya zakulo daya daga cikin ‘yan industirin wanda zai iya kawo ci gaba wurin kayan aiki, horar da darektoci da jarumai da sauransu.
Sai dai a cikin makon nan rade-radi yayi yawa dangane da batun aurensu da jaruma Rukayya Dawayya.
An samu tabbaci dangane da hakan ne ta wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram a ranar Juma’a 15 ga watan Yulin 2022.
Kamar yadda ta sanya a shafin nata mai suna DawayyaRukayya85, ta ce shi din amsa ne ga addu’ar da ta dade tana yi tare da kiransa masoyinta na gaskiya.
Kamar yadda ta wallafa hotonsa ta yi tsokaci a kasa inda tace:
Samun masoyin gaskiya a wannan zamanin da rashin gaskiya tayi yawa sai karfin addu’a. Alhamdulillah ya Rabbi, lakal hamdu wash shukur.
“Allah na gode maka da ka amsa addu’a ta. Khairun nas man yan fa un nass.”