Ancigaba da Daukar Shirin Izzar so Bayan Rasuwar Darakta Nura Mustapha waye

Ancigaba da daukar cigaban shirin izzar so bayan Rasuwar Darakta Nura Mustapha waye ayau Asabar 23/07/2022.

Bayan rasuwar marigayi Nura Mustapha waye wanda Allah yayimai rasuwa ranar Asabar 2/07/2022 da sanyin safiya, wanda rasuwarsa ta matukar girgiza masana’antar Kannywood da wajanta.

Tabbas masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood tayi babban rashi domin kowa ya shaidi Nura Mustapha waye mutum ne mai son addini mai kaunar manzon Allah haka zalika mutum ne mai girmama mutane.

Duk mai kallon shirin izzar so to tabbas ya karu dawani abu dangane da addini dakuma soyayyar Annabi Muhammad s.a.w kuma duk hakan tafaru ne ta dalilin Nura Mustapha waye.

Shirin izzar so shirine wanda shine na farko da akafi karkata akan soyayyar Manzon Allah dakuma abubuwan dasuka shafi addini wanda duk wani maikallon shirin idan ya kalla shirin dolensa saiyaga wani abu dazai karu dashi.

Yanzu haka munsamu wani gajeran faifan bidiyo wanda yake nuna yadda ake cigaba da daukar shirin, kamar yadda zakugani yanzu.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button