Masu kokawa kan fasinjojin jirgin kasa da aka kamasu munafukaine cewar Naziru sarkin waka

Naziru sarkin waka ya koka kan mutanen da suke fitowa suna koke kokensu kan mutanen da yan Bindiga suka kamasu tun watan maris akan hanyar Abuja zuwa kaduna a jirgin kasa.

Naziru sarkin waka ya bayyana cewar sai yan bindiga sun nuna hotunan mutanen kokuma faifan bidiyonsu sannan wasu mutane suke fitowa kafofin sada zumunta suyita kuka suna bayyana cewar basa iya bacci akan halin da mutanen suke ciki.

Ya kara da cewa mutanen dasuke hannun yan bindiga kimanin kwanaki 150 inda mutane sun dukufa wajan addu’a, haka zalika malamai da sunayin abubuwan dasuka dace dayanzu ansamu sauki gameda wannan lamuran.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button