DA DUMI-DUMI: Kashe Mu Raba Mu Keyi Da Jami’an Gwamnatin Nigeria, Cewar ~ Shugaban ‘Yan Bindiga

Wannan na zuwane bayan wata hira da akayi da kasurgumin dan fashin Dajinnan maisuna Abu sani wanda shahararren dan fashin dajine da garkuwa da mutane.

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai satar mutane a Jihar ya ce matsalar rashin tsaro na ƙara ta’azzara ne a arewacin ƙasar saboda an mayar da lamarin na neman kuɗi.

Abu Sani wanda shi ne ya jagoranci sace ƴan matan sakandaren gwamnati ta garin Jengeɓe a bara, ya faɗi hakan ne a wani shiri na musamman na binciken ƙwaƙwaf da BBC ta gudanar kan ayyukan ƴan bindigar.

“An mayar da abin neman kuɗi a wannan ɓangare, kowa kuɗi yake nema,shi ya sa harkoki suke lalacewa, tun daga manyan har zuwa ga ƙananan,” in ji ɗan bindigar.

“Su kuma jami’ai su ma gwamnati idan ana rikici ana tura mata da kuɗi, ka ga ta wannan ɓangaren suna samu ke nan.

“Mu ma ta nan duk da dai za a zubar da jini a yi kashe-kashe, amma kuma a yi ta yi haka nan.”

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button