Gwamnatin Nijeriya Ta Gaza Wajen Kuɓutar Da Mu, Ƴan Uwan Mu Ne Suka Karɓo Mu, Cewar Barista Hassan Usman

Daya daga cikin fasinjojin jirgin kasan da aka sace tun watan maris din shekarar 2022 yashaki iskar yanci bayan kubutarsa shida wasu mutum biyu daga hannun yan bindigar.

Cikin wata shira da yayi da BBC Hausa, Barista Hassan Usman, wanda ya samu kuɓuta daga hannun ƴan ta’addán da suka yi garkuwa da su tsawon kwanaki 120, ya bayyana cewar, ƴan uwansu ne suka kuɓutar dasu daga hannun ƴan ta’addán da sukayi garkuwa da su.

“Tun a kwanakin baya ƴan uwanmu suka je zasu kuɓutar damu, amma sai gwamnati ta hana, inda aka sa jami’an tsaro suka tare hanya, saboda haka sai jiya bayan bayyanar bidiyon da ƴan ta’addán ke dukan mu, sannan ne ƴan uwanmu suka samu damar wucewa suka kuɓutar damu mu uku.” Inji shi

Sai dai har ya zuwa yanzu babu wani bayani daga ɓangaren gwamnatin Nijeriya kan kuɓutar Barista Hassan Usman da sauran mutane biyu.

Gadai cikakken bidiyon yadda Barista Hassan Usman yayi bayanin yadda alamuran ya kasance.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button