Ansaki Mutum 5 daga fasinjar Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna da Yan Bindiga sukayi Garkuwa dasu
Masha Allah a jiyane cikin hukuncin ubangiji karin mutum 5 daga cikin wanda akayi garkuwa dasu a jirgin kasan kaduna zuwa Abuja tun watan maris din shekarar 2022.

Rahotannin da muke samu a yanzu ya tabbatar mana da cewa ƴan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasa na Kaduna sun ƙara sako mutun biyar daga cikin fasinjojin da suka yi garkuwa da su a hanyar jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna tun a ranar 28 ga Maris, 2022.
Daga cikin fasinjojin da aka ceto aƙwai, Farfesa Mustapha Umar Imam wanda likita ne a Asibitin Koyarwa na Jamilar Usman Ɗan Fodio da ke Sakkwato
- Akibu Lawal
- Abubakar Ahmed Rufa’i
- Mukthar Shu’aibu
- Sidi Aminu Sharif.
Anan zaku kalli wani faifan bidiyon hira da akayi dawasu daga cikin wanda yan bindigar sukayi garkuwa dasu.
Ga video
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.