Nayi wankin breziya da pant na Mata kafin Nasamu Daukaka a masana’antar Kannywood cewar Mustapha Naburaska
Shahararren jarumin a masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood Mustapha Naburaska cikin wata hira da akayi dashi acikin shirin gari ya waye ya bayyana irin wahalar dayasha kafin yasamu daukaka acikin masana’antar Kannywood.
Jarumin ya bayyana cewar a shekarun baya dasuka wuce ya matukarsha wahala hatta wankin breziya da pant yayi na jarumai mata domin kawai yasamu ya rufawa kanshi asiri a shekarun baya dasuka wuce.
Cikin hirar jarumi Mustapha Naburaska ya bayyana cewar akwai lokacin da akaje dashi wajan daukar wata waka inda aka roki wani darakta alfarma a sakashi acikin bidiyon wakar saidai Darakan yayi burus inda ya bayyana cewar bashida inda zai saka jarumi Mustapha Naburaska acikin wannan wakar.
Haka zalika jarumin ya kara bayyana cewar acikin tsofaffin jarumai mata yayi musu wanki da guga haka zalika yayi dan aiken sayo sigari duk a wancan lokacin, saidai yanzu rayuwa ta canja Allah yakawo masa daukaka.
Ga video
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.