Yan Arewan Da Suka Shiga Hannun Jami’an Tsaron Yankunan Yarbawa, Amotekun, Yayin Da Suka Cika Mota Za Su Ci-Rani A Ogere

Su Ma ‘Yan Arewarmu Ya Kamata Su Dinga Shiga Yankin Kudanci Akan Tsari Domin Su Suke Jawowa Ake Wulakanta Su.

Sau da yawa za ka ga direba ya dauko mutane sama da dari akan mota ba tare da binciken wadanne irin mutane ya dauko ba.

Rashin tsaro da ta’addanci sun yi yawa a Arewacin Nijeriya don haka ba laifi bane idan Yarbawa suka samar da tsarin da zai taimake su akan rashin tsaro, dole ne su yi binciken duk wani wanda zai shigo yankinsu, irin haka yakamata ‘yan Arewa su yi koyi domin saurin sakin jikin da muke da shine da yarda da mutanen da ba mu san su ba ya kara jefa mu cikin musifa.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button