Kalli video Yadda Ango Yayi Wuff Da Babbar Kawa Bayan Amarya Ta Bashi Ciwon Kai Ranar Daurin Aure

Wani alamari daya faru a garin mararraban Guruku dake jahar Nassarawa yabawa mutan mamaki inda wata budurwa maisuna Hafsat Danladi fa bukaci a dakatar da daurin aurenta dawani saurayi.

Saidai babu wanda yasan dalilin dayasa wannan budurwa ta bukaci a dakatar da auren nata da saurayinta, saidai hakan yasa wata daga cikin kawayenta maisuna zainab sa’id ta amince a daura Auren da saurayin kawar tata.

Daurin auren wanda da farko aka yi niyyar yi bayan Sallar Azahar, an bukaci jama’a su yi hakuri su sake komawa masallaci bayan Sallar la’asar, inda aka daura auren a lokacin bayan an tuntubi waliyyan sabuwar amaryar da kuma yi mata gwaje-gwajen kiwon lafiya.

Saidai rahotanni sun bayyana cewar Ango Sulaiman Musa ya suma bayan jin cewar Amarya ta bukaci a dakatar sa daurin auren nata dashi, inda bayan farfadowarsa ke fada masa cewar yanzu kuma da kawar Amarya za’a daura Auren maisuna zainab sa’id.

An gabatar da ita a gare shi, nan take ya ce ya amince. Sai dai wani abin mamaki shi ne yadda tsohuwar budurwar ta saki jiki ta fadi bayan samun labarin daura auren da wata,” inji shi.

Rahotanni sun bayyana cewar angon da tsohuwar budurwar ’ya’yan wa da kanwa ne kuma a gidan su angon ta tashi. Sai dai daga baya an ce ta danganta lamarin da aljannu tare da yin nadamar abin da ta yi.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button