Labari Da Dumi Duminshi Wani Matashi Ya Tsere Daga Kotu Bayan An Yanke Masa Hukuncin Zuwa Gidan Gyaran Hali Na Tsawon Wata Sha Takwas (18)

Matashi dai ya tsere daga cikin wata kotu bayan an yanke masa hukuncin ɗaurin watanni goma sha takwas (18) a gidan gyara halinka da tarbiyya sakamakon samun sa da aikata laifi a kasar Ghana.

Matashin mai shekaru 29 wanda Direban Mota ne, aka kawo shi harabar kotun hannunsa a ɗaure da Ankwa. Jami’an Yansandan ne suka gabatar da saurayin mai suna Shu’aibu Mohammed agaban kotu a ranar Larabar da ta wuce.

Bayan matashin ya cika wandon sa da iska ne jami’an tsaro da sauran suka bishi a guje dan sake Kamoshi a dawo dashi gaban kotun.

Matashin ya gudu ne ta kofar kotun wanda ya tsallaka babban Titi zuwa Kumasi cikin daji a Akokori-Kwadwo yayin da jami’an yan sanda da jama’a suka kama shi charaf..

Arewa Joint Ne Sukazo Muku Da Labarinnan..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button