Jarumar shirin finafinai na kannywood Fati shuuma ta bada shawararta ga yan mata masu shirin shiga harkar film ku shiga domin kallan video

Fati shu’uma sannanniyar jaruma ta masana’antar shawararta ga yan mata masu shirin shigowa harkar mu ta film itace su tsaya su nutsu tukunna kafin su shiga..

Jaruma a masanaantar kannywood mai suna fati shu’uma ta bayar da wasu shawarwari ga yam mata masu sha’awar shiga harkar film Wanda aka yaba da wannan shawarwarin data bayar harma wasu ke ganin wannan jarumar lallai bata da matsala a zahiri…

Tace duk wacce takeda sha’awar shigowa film tota kyautata niyarta sai Allah yasa mata albarka aciki sannan tace kar wacce ta shigo da niyar yin kudi kawai ta shigo idan tana da rabo zatayi domin abun rabo ne

Jarima fati shu’uma ta fawa mutane cewa bafa a kudi a iya harkar film sai an hada da wata harkar sannan asiri yake rufuwa duk da tace su a yanzu alhamdulillah asirunsu a rufe yake babu wani abu da suka rasa a wannan harkar ta film

Kuma ta kara dacewa ya kamata hukumar tace finafinai ta cigaba da lura da kananun jarumai sababbin zuwa shiga harkar film batare da sanin magabatan suba domin kiyaye musu hatsarin rayuwa nan gaba..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button