Kalli video Yadda wani matashi ya kashe Mahaifinsa saboda Yayiwa Mahaifiyarsa Kishiya
Kai Duniya ina zaki damu! Wani matashi Maisuna Kasim ya kashe mahaifinsa har lahira sakamakon kishiya da mahaifin nasa yayiwa mahaifiyarsa a garin suleja.
Dan uwan mahaifin maisuna isah ya bayyanawa yan jarida cewar kasim Muhammad yayi amfani da falanki inda ya bugawa mahaifin nasa, bayan aikata laifin kuma ya tsere.
Matashin wanda aka bayyanasa a matsayin Dan shaye shaye a cewar isah dan uwan mahaifin nasa ya bayyana cewar zai iya aikata abindama yafi hakan sabida shaye shayen dayakeyi.
Sa-in-sa tashiga tsakanin kasim da mahaifin nasa inda nan take kasim ya dauki falanki ya bugawa mahaifin nasa ganin yadda mahaifin nasa ya fadi hakan yasa kasim ya tsere.
Saidai bayan faruwar lamarin an dauki mahaifin kasim izuwa asibiti domin abashu agajin gaggawa saidai cikin ikon Allah ba’a samu nasara ba domin ana zuwa asibitin Allah yayimai rasuwa.
Saidai dan uwan marigayin isah ya bayyana cewar sun sanar da hukumar yan sanda akan lamarin. Inda suka binne gawar mahaifin kasim kamar yadda addinin musulunci yasa ayi. Allah yaji kansa da Rahama Amin.
Allah ubangiji ya kyauta.
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.