Innalillahi yanzu gaskiya ta bayyana gameda da rasuwar kamaye na shirin Dadin kowa

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood Dan Azumi Baba wanda akafi sani da kamaye dai anyita wallaha wasu hotunansa tare da bayyana cewar Allah yayi masa rasuwa.

Wannan labarin ya matukar tayar da hankalin masoyan jarumin inda wannan labari yasamo asaline a dandalin sada zumunta na Facebook.

Saidai wannan labarin ba gaskiya bane domin fitaccen jarumin dai yafito ya bayyanawa duniya cewar yananan lafiyarsa kalau bai mutu ba kuma babu abinda ya samesa.

Wannan bashi bane karo na farko da aka tabayiwa kamaye irin wannan, inda watanni biyu zuwa uku ma an bayyana labarin karya dake cewar jarumin ya mutu alhalin yananan da ransa da lafiyarsa.

Ayanzu zakuga wani gajeran bidiyon jarumi kamaye domin ya gamsar da mutane cewar yananan da ransa da lafiyarsa bai mutu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button