Jaruma Rahama Sadau Tacika Shekaru 29 da haihuwa
Fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood jaruma Rahama Sadau tacika shekaru ashirin da tara 29 da haihuwa kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram.

A jiyane dai jarumar take cika wannan shekaru kamar yadda ta wallafa a kafar sada zumunta na Instagram.

Inda abokan sana’arta sukaita yimata murna tareda addu’ar Allah ubangiji ya karo mata shekaru masu albarka anan gaba.

Haka zalika masoyan jarumar suma sunyita yimata addu’a dakuma fatan alkairi acikin rayuwarta tagaba.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.