Innalillahi wa’inna raji’un Allah yayiwa Sheik Hamza Muhammad Lawal Rasuwa – Allah yaji kansa da Rahama

Innalillahi wa’inna Ilaihi Raji’un. Dukkannin mai rai mamaci ne. Rahotanni dake shigowa Jaridar HASKEN SHIRIYA a halin yanzu na nuni da cewa Shehin Malamin nan na addinin Musulunci dake zaune a Kaduna, Shaikh Hamza Muhammad Lawal Badikko ya rasu.

Bayanai daga makusantan Shehin Malamin sun tabbatar da labarin rasuwar Malamin. Sai dai ba su fayyace ma majiyarmu yadda Shehin Malamin ya rasu ba kuma yaushe ba.

Ya zuwa hada takaitaccen rahoton nan, babu wata sanarwa a hukumance daga iyalan mamacin ko makusantansa kan rasuwarsa.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button