Jarumin Kannywood Daddy Hikima Zai Angwance Shida Amaryarsa a ranar 27/01/2023
Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood Adam Abdullahi wanda akafi sani da Daddy hikima zai angwance a sati mai zuwa wato 27/01/2023.

Babban producer a masana’antar Kannywood Abubakar bashir maishadda shine ya fara wallafa katin auren jarumin a shafinsa na Instagram.
Tabbas idan ana maganar matasa masu tasowa acikin masana’antar Kannywood dolene a saka Daddy hikima abale domin yafara samun daukakane tun a lokacin da aka fara haska shirin a duniya a shekarar 2020.

Har izuwa wannan lokacin jarumin yanaci gaba da samun daukaka, haka zalika kuma a kulluma yana kara samun tarin masoya. Allah ubangiji yabasu zaman lafiya a aurensu shida amaryarsa.
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.