Kalli video Hamisu breaker – Ban yaudari Rakiya Mousa ba – Hamisu breaker
Maganganu na kara rincabewa gameda faifan bidiyon jaruma Rakiya Mousa akan wata hira da akayi da ita wanda Hadiza Gabon take shiryawa.
Cikin hirar nema dai jaruma Hadiza Gabon ta tambayi Rakiya Mousa inda yake mata kaikayi nanfa take Rakiya ta fara bayyana irin kuncin datake ciki gameda da yaudarar dawani mawaki yayi mata wanda bazata manta da hakan ba.
Masoya dama wanda ba masoyan Rakiya Mousa ba sun matukar tausaya mata akan wannan lamari tare da bayyana irin nasu ra’ayoyin akan wannan alamari.
Saidai tuni wasu na gefen mawakin sunfito sun karyata wannan labari inda suke fadin ba haka gaskiyar maganar take ba.
Indama a gefe guda wasu suke bayyana cewar yakamata jarumar tayi hakuri da mawakin domin a halin yanzu yama riga yayi aure abinsa a boye babu wanda ya sani.
Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.