Wata sabuwa – Kotu ta tura Mal Abdul’aziz Dutsen Tanshi Gidan kurkuku

Kusan wata daya kenan da akaso ayi zama tsakanin malamin dawasu malamai a jahar bauchi dake arewacin najeriya kan zargin kalaman batanci dayayiwa annabi Muhammad.

Saidai daga baya kungiyar malamai ta jahar bauchi tasake fitar da takarda wajan dakatarda wannan zama daza’ayi da malamin tareda fadin cewar sai nan gaba zata sanar da wani lokacin na daban.

Saidai kwatsam yaudai muka tashi dajin rahoton yadda hukumar yan sanda ta gayyaci malamin inda daganan aka fadamai abubuwan da ake tuhumansa.

Wanda daga karshe dai ya musa aka mikasa zuwa ga kotu inda anan bayan zama alkali ya dage shari’ar zuwa ranar Talata.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button