Labarai

BABBAR MAGANA: Matasan N-Power Sun Baiwa Gwamnatin Tarayya Mako Guda Ta Biya Su Hakkinsu Na Tsawon Watanni Tara

Kungiyar masu cin gajiyar shirin Npower karkashin jagorancin shugaba Comrd Muhammad Habibu Abubakar GMB suna cigaba da yin kira ga gwamnatin tarayyar Nijeriya da sabuwar Minista Dr Betta Edua da su gaggauta biyan su hakkokin su.

Na ma’aikatan N-Power rukunin C hakkonkin su na watannin tara, ko su tsunduma zanga-zangar lumana a duk fadin kasar tare da hada gagarumar taron manema labarai a duk sassan fadin kasar a cikin nan da kasa da mako guda.

“Muna zuwa aiki ba a biyan mu hakkonkin mu. Kuma mun yi aikin wata da watanni ba tare da an biya mu ba, hakika matasan kasar mun cancanci kyakyawar karshe da kyakyawar fata.

Da sakamako sakamakon bautawa kasa na matasan na Npower”, cewar shugaban matasan na N-Power, Comrd Muhammad Habibu Abubakar GMB.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Get 1.5GB of Data For Free

X