Labarai
AUREN ZAWARAWA: An Samu Masu Ciki Da Cutar HIV A Wajen Gwajin Aure A Jihar Kano
A shirye-shiryen Auren Zawarawa a jihar Kano, hukumar Hizbah tace ta sami masu dauke da cutar Kanjama’u HIV da masu dauke da cutar Hanta nau’in Hepatitis B.

Haka kuma hukumar tace cikin gwaje-gwajen sun sami mata masu dauke da juna biyu.
Mai magana da yawun hukumar ta Hisbah, Lawan Fagge ya ce an gano wannan ne a wajen gwaje-gwajen da ake yi kafin auren.

Hukumar ta ce yanzu haka ta maye gurbin ire-iren su da wasu mutane daban, yayin da su kuma an fara basu magunguna da shawarwari don rabuwa da cututtukan.
Yanzu haka dai shugaban hukumar Hizbah reshen jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, yace shirye-shirye sun yi nisa na Auren.