Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Hudu Tare Da Tafiya Da Wasu A Zaria

Al’amuran tsaro a Arewa na cigaba da tabarbarewa, Rahotanni sun tabbatar da cewa a daren jiya Juma’a da misalin karfe 11na dare , masu garkuwa da mutane sun yi dirar mikiya a Anguwan Dankali yankin Dan Magaji dake Zaria.

Maharan sun je gidan Alh Musa, inda suka tafi da mata. Maharan dai sun dinga harbi ba kakkautawa ga wanda suka yi karo da shi. Inda aka tabbatar da sun kashe mutane hudu tare da ji wa wasu raunuka suna asibiti.

Ya zuwa safiyar nan an samu kiran waya daga matan da aka tafi da su cewa sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutanen amma ba su san inda suke ba.

Muna rokon Allah ya jikan wadanda suka rasu,
Ya kubutar da wadanda aka kama, sannan ya yi mana maganin ta’addanci da ‘yan ta’adda.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Get 1.5GB of Data For Free

X