Kannywood
Ba’a sakin Aure da kowanne irin Yare saida Larabci – Cewar Malamin Shi’a Sheik Abdullahi Dahiru
Wani kalamai na malamin shi’a maisuna Mal Abdullahi Dahiru ya matukar tada hazo inda ya bayyana cewar akwai kuskure wajan yadda mutane sukeyin saki.

Malamin shi’ar ya bayyana cewar ba’a sakin aure da kowani yare saida yaren larabci wanda wannan maganar tasa tasa mutane sunata tofa albarkacin bakinsu.
Saidai a gefe guda ansamu wasu sun goyi bayan maganar malamin inda suke fadin tabbas abunda ya fada dai dai ne.

Saidai kuma a gefe guda wanda suka nuna cewar malamin yayi kuskure sunfi yawa, inda suka bayyanar cewar addinin musulunci sauki garesa kuma yabada damar zaka iya sakin matarka da kowani yaren da kakeji.
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode sosai.